Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Saurayi yace budurwarsa ta biyashi duk abinda ya kashe mata bayan tace bazata aureshi ba

 Saurayi yace budurwarsa ta biyashi duk abinda ya kashe mata bayan tace bazata aureshi ba
Wata Budurwa ta koka saboda saurayinta yace ta biyashi kudin daya kashe mata yayin karatunta saboda tace bazata aure shi ba

Wani al'amari ya faru tsakanin wani saurayi da wata budurwarsa wanda suka jima suna tare tsawon lokaci wanda ya bawa mutane mamaki.


Al'amarin ya faru ne jim kadan bayan an hangi yarinyar tayi rubutu tana kokawa akan maganar da saurayin nata yayi mata na ta biyashi duk wani kudi nasa daya kashe mata, tun daga farkon haduwarsu har zuwa lokacin da ta gama makaranta tunda tace bazata aure shi ba.


Saurayin yace shi baiga dalilin da zaisa ya hakura da kudin daya kashe mata ba tunda dai tace bazata aureshi ba, domin dama saboda tace zata aureshi ne yasa yai ta mata wannan wahalar tunda suka hadu har zuwa wannan lokacin.


Ga yadda maganar ta kasance ma'ana yadda lamarin nasu yake

Wani saurayi da wata budurwa sun hadu tun shekarun baya wanda tun daga lokacin da suka hadu shi saurayin shine yake daukar nauyin karatun yarinyar tun daga secondary har jami'a, da yarjejeniyar zata aureshi idan ta gama.


Bayan ta gama karatun shine saurayin ya dawo mata da maganar da sukayi tun a baya wato batun aure tunda ta gama makaranta, to amma sai yarinyar ta kada baki tace ita aurenta dashi bazai iyuwa ba saboda yanzu ta shige ajinsa.


Da aka tambayeta me yasa bazata aureshi ba sai tace ita yanzu gaskiya me kudi take so wanda zai iya kula da ita kuma zai kula da yayan da zata haifa yadda zasu rayu cikin aminci suci mai kyau su kuma sha mai kyau wanda ta sani idan ta auri wannan saurayin nata duka bazata samu wadannan burukan nata ba saboda shi baiyi wani dogon karatu ba kuma sana'arsa ba wata babba bace domin bata kawo masa kudi sosai.


Wannan maganar da saurayin yaji yasa yace to dole sai ta biyashi duk wani abinda ya kashe saboda ba haka sukayi da ita ba tun farko.

Shin kunga laifinsa dan Allah?


Abinda yasa muka boye sunan shine saboda tsaro kuma ana yawan samun wannan damuwar cikin al'umma dan haka yasa bamu kama suna ba.

Post a Comment

0 Comments